Tsakure
Ana samun sauye-sauye a harshe ta hanyar bunƙasa da faɗaɗa da kuma
samun sababbin al’amurra cikinsa da sukan faru lokaci-lokaci. Harshe yana bunƙasa ne
sakamakon ƙaruwar yawan masu magana da shi.
Haka kuma yana samun naƙasu sakamakon raguwar ‘yan
asalin harshen da ke magana da shi. Wannan maƙala mai taken ‘Nazarin ƙirƙira da ma’anar wasu sunayen ‘yan ta’adda
a Arewa Maso Yammacin Nijeriya.’ Wannan maƙala ce da ta yi nazarin bunƙasar harshen
Hausa da aka samu dalilin ayyukan masu ta’addanci a
wasu yankunan Arewa maso Yammacin Nijeriya. Maƙalar ta yi ƙoƙarin fitowa
da wasu sababbin sunayen da ‘yan ta’adda suke kiran kansu da su waɗanda suka ƙirƙirawa kansu
domin amfani da su wajen sadarwarsu ta yau da kullum da kuma wasu sunaye da
mutane suke kiran su da su. Manufar maƙalar ita ce, tabbatar da bunƙasar da
harshen Hausa ya samu a dalilin ayyukan ‘yan ta’adda ta hanyar samar da ƙirƙirarrun sunaye
na gama-gari da ake kiran su da su da kuma sunayen da suke laƙabawa kansu
da kuma sunayen da ake yi masu. An yi amfani da ra’in ‘Dangantakar Harshe da Rikici’ (Language of Violence) na
Smith, Alison G. da wasu (2008), wajen gudanar da wannan bincike wanda yake
magana a kan sadarwa tsakanin ‘yan ta’adda da waɗanda ke yaƙar su. Ra’in ya bayyana cewa, idan aka yi
la’akari da kalmomin da ɓangaroirin
biyu ke furtawa, to akwai abubuwan da ake samarwa dangane da harshe da bunƙasarsa. Daga
cikin dabarun da aka yi amfani da su wajen tattara bayanan da aka rubuta wannan
maƙalar akwai; tattaunawa da ‘yan ta’adda da suka tuba da mutanen da
aka yi garkuwa da su domin neman kuɗin fansa, amma daga baya suka
samu ‘yanci, da ‘yan jarida da wasu ɗaiɗaikun mutane
da ayyukan ta’addanci suke aukawa a cikin yankunansu. Haka kuma da sunayen da
ake ji na ‘yan ta’adda a kafafen sadarwa da kuma hanyar sadarwa na rediyo da
talabijin da jaridu da mujallu ta intanet.
Fitilun Kalmomi: Ƙirƙira, Harɗantawa, Sunaye, Ta’addanci
DOI: 10.36349/zamijoh.2023.v02i03.009
author/Isah Sarkin Fada & Musa Abdullahi
journal/Zamfara IJOH Vol. 2, Issue 3