Hantsi Leƙa Gidan Kowa: Nazarin Rubuce-Rubucen Hausa a Jikin Abubuwan Hawa a Gari Minna

    Tsakure

    Wannan aiki mai taken Hantsi Leƙa Gidan Kowa: Nazarin Rubuce-Rubucen Hausa a Jikin Abubuwan Hawa a Gari Minna, ya yi nazari ne a kan yadda ake amfani da harshen Hausa a jikin abubuwan hawa wajen isar da saƙonni daban-daban a garin Minna. Aikin ya yi nazarin irin ci gaba da bunƙasa da wannan harshe yake samu a sanadiyyar waɗannan rubuce-rubuce. Harshen ya samu karɓuwa sosai a gun al’ummar wannan gari, inda har al’adu da adabin wannan harshe na Hausa shi ma ya ci gajiyar wannan tsari. Manufar wannan ta haxa da tattaro wasu daga cikin ire-iren waɗannan rubuce-rubuce, tare da yin nazarin ma’anarsu da fage da da kuma irin gudummawar da sukr bayarwa, wajen haɓɓaka harshen Hausa da al’adunta. An yi amfani da hanyoyin hira da direbobin abubuwan hawa masu ɗauke da rubuce-rubuce da kuma wasu al’ummar waɗanna gari, domin gano irin rawar da rubuce-rubucen ke takawa. An gano lallai rubuce-rubucen na taka muhimmiyar rawa wajen fito da wannan harshe tare da yaɗa al’adunta, har ma da, haɗa kawunan al’umma, domin ta hanyar fahimtar harshen kan haifar da soyayya da fahimtar al’adun juna, ga al’ummar duniya baki ɗaya, musamman mazauna garuruwa da ke da ire-iren waɗannan rubuce-rubuce..

    DOI: 10.36349/zamijoh.2025.v03i02.009

    Download the article:

    author/Abdullahi Umar & Amina Mustapha Yahaya

    journal/Zamfara IJOH Vol. 3, Issue 2

    Pages