Suturun Matan Hausawa Da Sauyesauyen Zamani A Yau

    Tsakure

    A wannan bincike mai suna “Suturun Matan Hausawa da Sauye-Sauyen Zamani”, an aiwatar da shi ne a kan sauye-sauyen da baqin al’adu suka yi tasiri a kan suturun matan Hausawa. Muhimman batutuwa da aka gina wannan bincike da su, sun haxa da yin waiwaye a kan ireiren suturun matan Hausawa na gargajiya, inda aka yi bayaninsu daki-daki kuma filla-filla. A wannan aikin an kalli waxansu abubuwan da suke haddasar da zamani aa cikin suturun matan Hausawa. Har ila yau a wannan bincike an fahimci matan Hausawa sun sami wasu nau’o’in suturun daban-daban sakamakon sauye-sauyen zamani ta fuskar suturun baqin. Sannan sakamakon bincike ya sa aka lura da waxansu hanyoyin da ake tunanin zamani ya yi tasiri a kan suturun da matan Hausawa suka rabauta da su masu tsari da kuma akasin haka. An zavi a xora wannan bincike bisa ra’i na mazhaban sauyin al’adu. Daga qarshe sannan an lura a yau mata musamman ‘yan mata suna sha’awart suturun zamani fiye da ta gargajiya, saboda jan hankalinsu sosai. Kai taye wannan bincike ya kuma lura sosai wasu daga cikin nau’o’in suturun gargajiya sun tasamma vata ko salwanta a wannan zamani ko lokaci mai ci.

    DOI: 10.36349/zamijoh.2025.v03i02.008

    Download the article:

    author/Rukayya Muhammad Garba

    journal/Zamfara IJOH Vol. 3, Issue 2

    Pages