Tsakure
Tun gabanin Hausawa su karɓi kowane saukakken addini mata suke da kima a wurinsu. Manufar tabbatar da wannan hasashe shi ne ya ja hankali aka gudanar da ƙwarya-ƙwaryan nazari saboda a ƙyallaro shi a cikin al’adun matakan rayuwar Maguzawa na aure da haihuwa da mutuwa. Takardar ta yi amfani da karance-karance a matsayin hanyar bincike. An ɗora nazarin a kan tunanin Hausawa da yake cewa: “Inda aka san darajar goro nan ake nema masa ganye.” Takardar ta yi garkuwa da wasu misalai na al’adun Maguzawa guda goma sha biyar (15) waɗanda suka ratsi matakan rayuwarsu na aure da haihuwa da mutuwa; saboda a tabbatar da kimar da mace take da ita a wurinsu. Wasu daga cikin sakamakon da aka iya hangowa a dalilin wannan bincike sun haɗa da: Sanin kimar mace tare da tabbatar da ita a aikace da Maguzawa sukan yi, ya taimaka ta fuskokin ɗorewar tarbiyarsu da kyautatuwar zumuncinsu da tausaya wa junanusu tare da haɗin kan da yake tsakaninsu. Bugu da ƙari, wannan nazari ya gano cewa, kimar da mace take da ita a al’adun Maguzawa ita ce ta yi tasiri matuƙa har ya zuwa bayan da wasunsu suka karɓi addinin Musulunci. Ke nan, wannan ya tabbatar mana da abin da Hausawa suke cewa: “Daɗin goyo shi ke sa jijjiga.”
Keɓaɓɓun Kalmomi: Kima da Mace da kuma Matakan Rayuwa.